Magoya bayan gwamnan Kano Abba Kabir sun gudanar da zanga-zangar lumana a cikin birnin Kano
Daga Ɗanlami Malanta
Magoya bayan gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf, sun gudanar da zanga-zanga a cikin birnin Kano a yau Litinin.
Zanga-zangar ta samu halartar manyan mutane da suke yin tir da Allah wadai kan hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar kan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
Ce-ce-ku-ce dai ya kunno Kai a birnin mai mutane sama da miliyan 15 biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara da ta yi wanda kuma hukuncin ya sha banban da hukuncin da ya ke rubuce a jikin takarda.
A wani mataki na hadin gwiwa, a yau Litinin tsakanin karfe sha biyu zuwa karfe 1 na rana, dimbin masu zanga-zangar sun mamaye wurare masu mahimmanci a cikin birnin yayin da suka ziyarci wurare da dama, inda suka mamaye Titin Kano zuwa Zaria, titin Maiduguri ta hanyar babbar gadar Hotoro, da Kanti Kwari (Kasuwar masaku ta Kano).
Daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne tare da kiran a yi wa Abba Kabir Yusuf adalci.
Masu zanga zangar sun daga kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce kamar haka: “Kano my city my state”, “Justice for Kano”, “Justice for Abba”, “An saci wa’adin Abba a shekarar 2019, ba za mu bari hakan ya faru a 2023 ba.”
Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da ‘yan sanda suka gano cewa “wasu kungiyoyi marasa son zaman lafiya sun dukufa wajen kawo tashin hankali a jihar”, yayin da suka jaddada cewa ‘yan sanda na sa ido kan lamarin.