Magoya Bayan Guinea Guda 6 Sun Rasa Rayukansu Yayin Murnar Samun Nasara
Daga Sabiu Abdullahi
Magoya bayan tawogar ƙwallon ƙafar Guinea guda shida ne suka mutu a lokacin da suke kina farin cikin samun nasara a wasan farko da suka samu a gasar cin kofin Afrika.
Feiguifoot, wadda ita ce hukumar kwallon kafa ta Guinea, ita ta tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin.
Ta ce lamarin ya faru ne a yayin bikin murnar da aka yi a titunan Conakry, babban birnin kasar.
Idan mai karatu bai manta ba a halin yanzu ana ta gudanar da gasar cin kofin Afrika a Ivory Coast.