Ma’aikatan MDD Sun Yi Zanga-zanga Kan Yanke Musu Kudade da Sallamar Abokan Aikinsu

Daruruwan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis a gaban shelkwatar kungiyar ta nahiyar Turai, suna nuna rashin jin daɗinsu kan sallamar ma’aikata da aka fara yi sakamakon gagarumar matsin kudade daga gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka da wasu masu bayar da tallafi.
Masu zanga-zangar sun rike alluna da ke ɗauke da rubuce-rubuce kamar “A daina korar ma’aikatan MDD yanzu!” tare da rera taken “Ma’aikatan MDD ba kaya ba ne!”
Rahotanni sun bayyana cewa yanke kudaden zai fi shafar sassan da ke dogaro kacokan da tallafin da ba na doka ba, musamman daga Amurka wacce ita ce tsohuwar babbar mai tallafi.
Daga cikin waɗannan sassa har da Shirin Ciyar da Duniya (WFP) da Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).