December 7, 2025

Ma’aikatan hukumomin sufurin jiragin ruwa sun samu ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa ₦200,000

images (9) (17)

Daga Abdullahi I. Adam

A wani taro da aka gabatar ranar Asabar a Legas ne hukumomin sufurin jiragen ruwa na ƙasa tare da ƙungiyar ma’aikata mai suna “Shipping Agencies, Clearing, and Forwarding Employers Association,” SACEFA suka amince da biyan mafi ƙarancin albashi na ₦200,000 ga ma’aikatansu.

Taron rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin SACFEA da ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta “Maritime Workers Union” da ƙungiyar masu safarar jiragen ruwa ta Najeriya an shirya shi ne tare da goyon bayan ma’aikatar kula da harkokin jiragen ruwa, wanda ke zuwa bayan shekaru 20 na gwagwarmayar ganin an samar wa ma’aikatan da albashi mai gwaɓi.

Da take jawabi yayin bikin rattaba hannu kan takardar a ranar Asabar a Legas, Shugabar ƙungiyar ta SACFEA, Misis Boma Alabi (SAN), ta bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashin nasu zai kasance mafi girma a tsakanin masana’antu a faɗin Najeriya.

“Abin da ya fi muhimmanci shi ne, wajen samar da mafi ƙarancin albashi ga harkar sufurin jiragen ruwa, mun wuce duk wata ma’aikata a Najeriya. Mafi ƙarancin albashi na ƙasa shi ne ₦70,000, kuma mun san abin da aka dauƙa don ganin Gwamnatin Tarayya ta kai ga wannan matakin.

“A yarjejeniyar da muka ƙulla a yau, mafi ƙarancin albashinmu shi ne ₦200,000. Kusan ya ninka mafi ƙarancin albashi na ƙasa,” inji ta.

Ta ce a yayin da ma’aikatan na jiragen ruwa ke neman ₦160,000, sai ga shi mahukunta sun haura sun amince da ₦200,000, “saboda sun fahimci halin da ƙasar ke ciki kuma suna son ganin kowa ya yi farin ciki. Ba kawai muna son ma’aikata su rayu ba, a’a so mu ke ma’aikatanmu su yi aiki sannan su adana wani abu domin makomarsu.”

Alabi ta bayyana fatanta cewa sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wa bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasar ta hanyar daidaita daidaito tare da mafi karancin ma’auni da ingantaccen aiki da inganci.

Shi ma da yake nasa jawabin, Ministan harkokin ruwa da tattalin arziƙi na ruwa, Adegboyega Oyetola, ya shawarci ma’aikatan da ke kula da harkokin sufurin jiragen ruwa da su ƙara ƙaiimi da ƙwazonsu domin nuna godiya kan wannan tagomashi da hukumomi suka masu.

“Ina kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su dage da jajircewa wajen bayar da shawarwarin kare haƙƙin ma’aikata ta hanyar tabbatar da bin ƙa’idojin da aka amince,” inji Oyetola.

Haka nan kuma, ministan ya ƙara da cewa gwamnati za ta cigaba da ba da kulawa ta hanyar samar da yanayin da ya dace tare da kuma cigaba da ingantawa lamuran ɓangaren na sufurin ruwa.

“Yayin da muke ci gaba, ya zama wajibi dukkan masu ruwa da tsaki su kiyaye ka’idojin wannan yarjejeniya. Ina kira ga masu daukar ma’aikata a cikin masana’antar da su rungumi wadannan yanayi a matsayin wani abin da zai karfafa yanayin aiki mai kyau,” in ji Ministan.