Maƙala: Ya kamata ka amfanar da kanka daga lokacin da kake da shi
Daga Abdullahi Lawan Idris
A cikin awoyin (Hours) da muke yi a kasuwa, a wajen aiki, sau nawa ka taɓa yin tunanin cewar ni ma ya kamata na ba wa kaina lokacin da zan yi tunani, ko lokacin da zan koyi wani sabon abu na daban.
Misala na fita kasuwa, ko wajen aiki ƙarfe takwas (8:00 am) na safe, ba zan dawo gida ba sai karfi biyar na yamma (5:00 pm). Daga lokacin da na bar gida, lokacina ya zama na wasu ba nawa ba.
Shin kamar yance suma zasu amfana da lokaci na, nima zan iya amfanar da kaina lokaci na?
Za ka iya amfani da wayarka wajen sauraron “audio book.”
Misali, na san wani malami dan ƙasar “America” mai suna “Sheikh Khalid” akwai wata lecture da ya taba yi mai suna “The Purpose Of Our Life” kullum sai na saurara kuma na amfana.
Ka ga ke nan, wasu na amfanar lokacina, ni ma ina karawa kaina ilimi.
Akwai wane da na sani kullum in za mu haɗu, zan gan shi yana karatu.
Rana tsaka ya tambaye ni a kan yana son ya ga ya canza lokutan karatu saboda ya fahimci kamar yana ba wa kansa wahala ne.
Tun daga lokacin da na ba shi shawara da ya tsarawa kansa “time management”, har zuwa yanzu ban ƙara ganinsa ba.
Ko sati biyu ba a yi ba, wani bawan Allah ya tambaye ni, ya ce, “kana da lokaci?”
Na ce, na karatu? Wai daga wannan maganar har ya yi zuciya. Sai na gani cewa babu “emotional intelligence” wannan lamarin.
Duk da yawan amfani da waya (phone) yakan hana mutum yin wasu abubuwa, amma daga lokacin da ake amfana daga lokacinka, kai ma za ka iya amfani da wayarka wajen ganin kai ma ka amfanar da kanka.
Babu damar karanta littafi a wajen aiki, amma akwai damar amfani da waya a wajen aiki. Tun da hakane. Zaka iya karanta “PDF” a lokacin da kake zaune a wajen aiki, kafin ka dawo gida, ka ɗauki “hardcover” ka karanta.
Ba na mantawa har a cikin abin hawa, na sha karanta “soft copy” ba don komai ba, sai don na ga na amfana da wani abu daga cikin lokacina, domin Bature yana cewa; “Value your time”.
Abdullahi Lawan Idris ne ya rubuto mana wannan maƙala. Za a iya samunsa a wannan lamabar: 09167379342.