Limamai a Saudiyya ba za su yi dogayen huɗubobi a salloli gobe ba don zafin rana
Daga Abdullahi I. Adam
Babban limamin Harami, Asshaikh Abdurrahman Al-Sudais, ya ba da sanarwar cewa limamai su gajarta huɗubobi da sallolin da za a gabatar a gobe Juma’a.
Kamar yadda babban limamin ya ambata, wannan umurni ya biyo bayan tsananin zafin rana da ake fama da shi ne a ƙasar wadda a yanzu haka take cike maƙil da maniyyata.
Sanarwar wadda aka wallafa a shafin Facebook na “Inside the Haramain” na zuwa ne daidai lokacin da hukumomi a ƙasar ke cigaba da samar da hanyoyin kula da mahajjata waɗanda wasunsu ba za su iya jure ma irin zafin rana da ake yi a ƙasar ba.
Hey there this iis kinda of off topic but I was wondering
if blogs use WYSIWYG editors or if you have to
manually code with HTML. I’m starting a blog soon bbut have no coding skills so I wanted to get advice from someone with experience.
Any help would be greatly appreciated! https://ukrain-Forum.biz.ua/