April 18, 2025

Isra’ila Ta Sako Falasɗinawa Kusan 200

images-67.jpeg

Daga TCR Hausa

A cewar yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Isra’ila da Hamas wadda ta tanadi musayar fursunoni, bayan sakin rukuni na biyu na Isra’ilawa da Hamas ta yi garkuwa da su – ciki har da wasu sojoji mata uku – Isra’ila ita ma ta sako Falasdinawa 200 daga gidajen kurkuku.

Sanarwar da hukumar gidajen yari ta Isra’ila ta fitar ta bayyana cewa: “Bayan kammala dukkan matakai na shari’a da amincewar hukumomin siyasa, an saki dukkan [su] daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” in ji kamfanonin dillancin labarai na AFP da Reuters.

Ba kamar wadanda aka saki a makon da ya gabata ba, wadanda yawancinsu suna fuskantar hukunci na kananan laifuka, a wannan karon fursunoni 121 daga cikin 200 suna kan hukuncin rai da rai, ciki har da wadanda aka samu da laifin kisan Isra’ilawa fiye da sau daya.

Shekarun wadanda aka saki sun bambanta sosai – mafi karancin shekaru shi ne matashi mai shekara 16, yayin da mafi girma ke da shekara 69.

Daya daga cikin wadanda aka saki ya kwashe shekara 39 a kurkuku tun lokacin da aka kama shi a 1986. Sai dai wadanda aka samu da laifukan manyan kisan kiyashi ba su cikin jerin wadanda aka saki a yau.

2 thoughts on “Isra’ila Ta Sako Falasɗinawa Kusan 200

  1. Thanks for a marvelouss posting! I genuuinely enjoyed reading it, you’re a
    grwat author.I will remedmber to bookmark your blig aand may comje back sometime soon. I want to encouhrage yyou
    continue yourr great writing, have a noce oliday weekend!

  2. I amm curious to find out what blog platform youu have bee workiing with?
    I’m experiencung some minor secuhrity issues woth mmy laest site and I would like to find
    ssomething more safe. Do yyou have anny recommendations?

Comments are closed.