LGBTQ+: Majalisar wakilai ta nemi a dakatar da yarjejeniyar Samoa
Daga Sabiu Abdullahi
Majalisar wakilan Najeriya ta nemi gwamnatin tarayya ta yi gaggawar dakatar da yarjejeniyar Samoa da ta hanyar ka-ce-na-ce.
Majalisar, a zaman da ta yi yau Talata, ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai gwamnati ta fito ta bayyana ɓangarorin yarjejeniyar da suka haifar da hatsaniyar.
Ɗanmajalisar wakilai Hon Aliyu Madaki ya bayyana wannan yunkuri wa manema labarai, inda ya ce majalisar ta kuma nemi ministocin da suka jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar su gurfana gabanta tare da takardun yarjejeniyar domin buƙatar fayyace komi musamman “ɓangaren da ke bayani kan daidaiton jinsi.”
BBC ta rawaito cewa yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanya wa hannu da Tarayyar Turai ta tayar da ƙura a Najeriya inda wasu ƴan ƙasar da dama suka nuna fushinsu musamman zargin cewa yarjejeniyar na ƙunshe da wani ɓangare da ke nuna goyon baya da kuma kare muradun masu maɗigo da luwaɗi.
Sai dai tuni gwamnatin tarayya ta ƙaryata wannan zargi, inda ministan kasafin kudi da tsare-tsare da kuma ministan watsa labarai suka ce Najeriya ba za ta taɓa amincewa da wata yarjejeniyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma al’adu da addinin ƙasar.