January 15, 2025

Lallai na koyi darussa lokacin da nake zaman gidan yarin Kuje—Jolly Nyame

3
Jolly-Nyame.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, ya yi alkawarin zama shugaba nagari idan aka sake ba shi damar gudanar da al’amuran jiharsa.

Nyame ya yi wannan alkawarin ne a yayin bikin godiya da ya gudana a sakatariyar kungiyar Kiristocin Najeriya da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Tsohon gwamnan wanda ya ce ya koyi abubuwa da dama daga zaman gidan yari, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa afuwa a shekarar 2022 bayan da aka same shi da laifin zamba a shekarar 2018.

Ya shafe shekaru hudu ne kawai na hukuncin daurin shekaru 14.

3 thoughts on “Lallai na koyi darussa lokacin da nake zaman gidan yarin Kuje—Jolly Nyame

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *