January 14, 2025

Labari yadda wani miji yake gallaza wa matarsa saboda rashin haihuwa

0
IMG-20240901-WA0026

Rubutawar Hicham Azguid Ɗan kasar Marocco

Fassarar Auwal Albarudy

Tunanina shi ne cewa mace tana fara rayuwa ne lokacin da aka fara kiranta ““maman wane ko wance.”

Haka shi ma namiji ana cewa ya shigo duniya lokacin da ya angwance. Don haka mahaifata take mararin jaririn da zai fito duniya a raɗa min sunan uwa kamar kowacce mace.

Haka mijina ya yi tarayya da ni a wannan fata, amma hakan ba zai kasance ba sai ta hanyar aure da zai haɗe zuƙata biyu su zama ɗaya.

Me ya sa nake wannan tunani haka? Yau aurenmu ke cika shekara takwas—shekaru bakwai sun gabata a rayuwar aurena da Ali Wanda makwabcinmu ne tun yarinta don haka mu abu biyu ne tamkar daya, haka dai nake tsammani.

Shekarar farko a aurenmu cike take da so, ƙauna da kyakkyawar fata, amma alamu sun gwada sharar fage suke wa cakuɗaɗɗun shekaru.

Shekaru bakwai na yi ina zirya tsakanin likitoci da suka ƙware kan sabubban rashin haihuwa, kuma duk sakamakon ya tabbatar ba ni da matsala kuma zan iya haihuwa da izinin Allah, to mijina fa?

Shi kam ya ƙi yarda a gwada shi balle ya san matsayinsa kamar dai ya na tsoron sakamakon ya fallasa cewa matsalar daga shi ne, don haka gallazawarsa ta tsananta, ya ci gaba da ɓoye matsalarsa a bayan tawa—haushi da muzgunawa yake min kullum.

Mijina ya san ni sarai kuma ya ƙware wajen iya amfani da raunina da ƙarancin wayona a matsayina na mace, yana hukunta ni kan laifin rashin haihuwa da wani salon na daban, yana tozarta ni kan laifukan da ba su taka kara sun karya ba.

Hatta kan ƙananan abubuwa kamar sukari ko gishiri idan hannuna ya zarce a girki, haka zai ci min zarafi, har ma idan ya nemi rigarsa bai gani ba duk da shi ya ajiye ta da hannunsa.

Haka nake jure duk gallazawarsa da muzgunawa da kome, duk saboda jaririn da bai zo ba.

Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba yana korata daga gidansa, yan unguwa da yan’uwa ne ke shiga tsakani su roƙe shi ya dawo da ni, sai ya dawo da ni amma bisa sharaɗi uku: na farko hannuna ya ƙware wajen kintata gishiri, sukari da yaji, sannan harshena ya gwanance wajen ɗanɗana miya, na karshe mahaifata ta tabbatar ta ɗauki ciki.

Bayan haka ta faru da mako ɗaya ya min korar kare—na gode wa Allah bai sake ni ba. Saboda ƙarfi da ƙarar rufuwar kyauren sai da jiri ya kamani na fadi ƙasa, aka yi gaggawanr kai ni asibiti.

Likita ya ce nutsuwa da kwanciyar hankali nake buƙata sakamakon labarin da ya samu a kaina.

Bayan an yi gwaje-gwajen da suka dace, likita ya sanar da ni labari mai daɗin ji wanda ban yi tsammaninsa ba a wannan lokacin.

Ya ce, “Ki na da juna biyu kuma za ki haifi mace ko namiji da izinin Allah.”

Kamar an sihirce shi, yanayin mijina ya sauya gaba ɗaya, ya mayar da ni gida yana rantsuwa cewa ba zai sake wulakanta ni ba har abada.

Na ɗaura tafukana a kan cikina kai kace magana nake da kyautar Allah da ba ta gama kammaluwa ba.

Na ce, “Na jure gallazawa saboda kai haka kuma zan jure ɗawainiyar kula da kai bayan zuwanka.”

Sai wani sauti ya nufo daga nesa ana cewa “Hadiza! Hadiza, kina Ina? Baƙi suna jiranki.”

Na ce ga ni nan zuwa, Yaya Ali!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *