February 10, 2025

Labarin Asalin Ƙabilun Kwandon Ƙaya Da Ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi

0
IMG-20241108-WA0010.jpg


Daga Rabiu Toro

Littafin Malam Ibrahim Sabo Gumau mai suna Ƙasar Lame A jiya da Yau, wanda aka wallafa littafin a shekara ta 2021, ya ƙunshi tarihin ƙasar sarkin yaƙi (Lame), yadda aka samar da ƙasar, sarakunan da suka mulki ƙasar, da kuma sassanci daga shekara 1812 zuwa 2021.

Malam Sabo Gumau ya ba da labarin asalin ƙabilun Kwandon Ƙaya wanda suke ƙabilu ne na kudancin Bauchi.

Suna daga cikin ƙabilun da suka taimaka wa sarkin Bauchi Malam Yakubu a ƴaƙinsa da Shehun Barno Kalumbo (Shehu Laminu ko El-kanemi) a shekarar 1827 a kan rashin fahimta tsakanin Kalumbo da Ɗanfodiyo na aukawa Hausawa da Kalumbo yake bayan kasancewarsu Musulmi. 

Sarkin Msulmi ya umarci Malam Yakubu ya ƴaki kalumbo. Yakubu kuma ya tattauna da sarakunan yankinsa a kan umarnin da Sarkin Musulmi ya ba shi, suka amsa baki ɗaya cewa sun amince sun yarda ya bi umarnin Sarkin Nusulmi.

Bayan dawowar Yakubu Bauchi ya sa aka tara masa ƙabilun ƙudancin Bauchi, Maguzawa da ke zaune bisa duwatsu a kan su gangaro daga dutsen fanshanu.

A daidai lokacin da Maguzawan za su gangaro, sai shugabanninsu suka ce tun da ba a ƙirga su an san yawansu ba, sai duk wanda zai gangaro ya sauko da dutse a hannunsa don su tara a waje guda, don idan sun dawo kowa ya ɗau nasa, za su san yawan wanɗanda aka kashe cikinsu.

Shi.ne asalin duwatsun nan da za a gan su a tare a gefen hanya, kusa da dutsen Fanshanu.

Wato yawansa shi ne waɗanda suka gangaro daga dutsen.

Wannan shine ɗan kaɗan, daga tarihin Kwandon Ƙaya (Grain of Stone) da.ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Rabiu Toro ya rubuto wannan maƙala daga karamar hukumar Toro da ke Jihar Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *