LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Shugaba Tinubu ya gana da manyan ƴan kasuwa kan matsalar tattalin arziki
Shugaba Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da manyan ƴan kasuwa a ƙasar tare da wasu gwamnoni.
Wannan tattaunawa dai ta ta’allaka ne kan yadda za a magance matsalar matsin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.
BBC Hausa ta rawaito cewa cikin waɗanda suka halarci taron akwai Aliko Dangote, Abdul Samad Rabi’u, Tony Elumelu da gwamnonin jihohin Ogun da Anambra.