May 17, 2025

LABARI CIKIN HOTUNA: Asibitin Bauchi yana buƙatar ‘ceton gaggawa’—rufi ya lalace, cunkoso ya yi yawa, babu isassun ma’aikata…

images (11) (18)

Daga Sabiu Abdullahi

Kiwon lafiya yana da matuƙar mahimmanci ta yadda babu wata gwamnati da ke da alhakin kula da shi ba tare da nuna kulawa ba, in dai har ba ta so a samu matsala.

A ƴan kwanakin baya, jaridar TCR ta ci karo da hotuna da bidiyo masu tayar da hankali da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna halin da asibitin kwararru na jihar Bauchi ke ciki.

Wannan ya sa muka gudanar da bincike, inda wakilinmu ya gano cewa rufin wani ɓangare na asibitin na yoyo, wanda hakan ya kai ga jiƙewar cikin asibitin tare da lalacewa [duba hotuna da bidiyon da aka makala].

Wannan ya nuna yadda ya zama dole marasa lafiya da ma’aikata su yi tafiya a hankali a cikin waɗannan wurare da suka lalace, saboda suna iya zamewa.

Rashin Tsafta

Wasu sassan asibitin ba su da tsafta, ga datti da ake gani a ƙasa, wanda hakan ke haifar da yanayi da zai iya sawa a ƙara kamuwa da cututtuka.

“Abin takaici ne kuma abin kunya,” in ji wani ma’aikacin lafiya, wanda ya ce a sakaya sunansa.

“Muna yin iya ƙoƙarinmu, amma yanayin yana da wahala a ba da kulawar da ta dace.”

Akwai Cunkoso

Asibitin kullum a cike yake maƙil, inda majinyata suke ta kwararowa. Wannan yanayi na rudani yana nufin cewa marasa lafiya ba sa samun kulawar da suke buƙata.

“Muna yin abubuwan da suka fita daga layinmu ma,” ma’aikacin lafiyar ya bayyana.

“Muna buƙatar ƙarin ma’aikata da kayan aiki don magance matsalar.”

Wannan cunkoson na ƙara yiwuwar kamuwa da cututtuka, yana kara jefa majinyata da ma’aikata cikin hadari, duk da ikirarin da gwamnan ya yi na daukar ma’aikatan lafiya kusan 3,500 a fadin jihar.

Alkawuran da ba a cika ba: An yi watsi da ceton gaggawa a fannin lafiya

Gwamna Bala Mohammed Abdulqadir ya taba yin alkawarin gina karin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko tare da ayyana dokar ta baci a fannin kiwon lafiya.

Amma duk da haka, halin da ake ciki yanzu ya ba da wani lamari ne na daban.

Kayayyakin aikin asibitin na ci gaba da lalacewa, kuma ma’aikatansa suna ci gaba da yin aiki fiye da kima kuma ba su da kayan aiki.

“Muna sa ran asibiti mai daraja ta duniya, amma a maimakon haka, mun sami ‘yan gyare-gyare ne kawai ga tsohon wurin,” in ji wani ma’aikacin asibitin, wanda shi ma ya nemi a sakaye sunansa.

Marasa lafiya a cikin haɗari: Ana buƙatar matakin gaggawa

“Da alama mummunan halin da asibitin ke ciki yana yin illa ga marasa lafiya. Suna fuskantar haɗarin kamuwa da cuta, kuma cunkoson yana nufin ba sa samun kulawar da suke buƙata.

“Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar mataki,” in ji ma’aikacin lafiyar.

“Asibitin yana buƙatar gyara cikin gaggawa, kuma ma’aikatan suna buƙatar horarwa da kayan aikin da suka dace don ba da kulawa mai inganci,” a cewarsa.

Babu haske

Halin da ake ciki a asibitin kwararru na jihar Bauchi yana da “ban takaici,” a cewar ma’aikacin

Idan ba tare da gaggawar sa hannun gwamnati ba, asibitin zai ci gaba da lalacewa, tare da jefa rayuwar marasa lafiya cikin haɗari.

“Muna fatan gwamnan zai cika alkawuran da ya dauka kuma zai zuba kuɗi a fannin kiwon lafiya,” in ji wani mahinyaci, wanda ya bayyana cewa a ɓoye sunansa.

“Rayuwar ‘yan kasa ta dogara da shi, yanayin asibitin yana nuna abubuwan da gwamnati ya kamata ta sa a gaba, kuma lokaci ya yi da za su dauki nauyi.”

Yunkurin jin ta-bakin gwamnati ya ci tura

Kafar TCR Hausa ta yi yunkurin jin ta-bakin wani jami’in gwamnatin Jihar Bauchi amma hakan ya ci tura.