Kylian Mbappé ya koma Real Madrid
Daga Sabiu Abdullahi
Kylian Mbappé ya kulla yarjejeniya da Real Madrid a hukumance, inda kungiyar za ta sanar da fitaccen dan wasan na Faransa a matsayin sabon dan wasanta a mako mai zuwa.
A cewar majiyoyi, “An sanya hannu kan kowane takarda, an gama, an kammala,” wanda ke tabbatar da matakin Mbappé na shiga kungiyar ta Siplfaniya.
Dan wasan mai shekaru 24 ya yanke shawarar ne a watan Fabrairu kuma tun daga lokacin ya kammala duk matakan da suka dace don canja wurin.
Wata majiya ta bayyana cewa: “Za a iya daukarsa a matsayin sabon dan wasan Real Madrid.”
Sayen Mbappé na zuwa ne a daidai lokacin da Real Madrid ta lashe gasar zakarun Turai, wanda ya zama tarihi a kungiyar.
Ana sa ran fitar da sanarwar a mako mai zuwa, wanda zai tabbatar da matsayin Mbappé a tarihin Real Madrid.