Kylian Mbappe na shirin komawa Real Madrid
Daga Sabiu Abdullahi
Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa Kylian Mbappe ya zabi komawa Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.
Jaridar Le Parisien ta bayyana ta sake wannan labari cikin wani rahotanta.
Rahoton na Le Parisien na ranar Asabar ya jefa fargaba a shafukan sada zumunta, yana mai cewa, “Babban Tauraron Faransa zai shiga babban kulob a duniya a kakar wasa mai zuwa.”
Magoya bayan Madrid suna cike da kyakkyawan fata yayin da tattaunawar ke gudana, da nufin tabbatar da abin da zai iya zama mafi kyawun kwangila ga Mbappe.