Kungiyar Musulmi Ta Garzaya Kotu Bayan Gwamna Ya Ɗanƙa Makarantun Gwamanti Ga Cocin Katolika A Edo
Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar Edo Muslims for Good Governance (EMGG) ta kai gwamnatin jihar Edo kara a kotu saboda kudirinta na bai wa Cocin Catholic wasu makarantun gwamnati.
A cikin karar da aka shigar mai lamba HAG/15/2025, kungiyar ta kalubalanci tsarin, tana mai cewa ya saba wa kundin tsarin mulki na 1999, wanda ya tanadi ‘yancin addini da kare bambanci.
EMGG ta ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ba tare da tuntubar shugabannin Musulmi ko sauran kungiyoyin addini ba.
Makarantun da abin ya shafa sun hada da St. Maria Goretti Girls Grammar School a Benin, Annunciation Catholic College a Irrua, St. Angela’s Girls Grammar School a Uzairue, da Obaseki Primary School a Benin.
Kungiyar ta ce tana adawa da wani shiri na mika karin makarantun gwamnati 36 ga Cocin Catholic, tana kiran matakin wariya ne wanda ba ya da sahalewar majalisar dokoki.
EMGG ta roki kotu da ta dakatar da gwamnatin Edo daga mika kowace makarantar gwamnati ga wata kungiya ta addini ba tare da bin ka’ida da yin adalci ga dukkan bangarorin addinai ba.
A zaman kotun, lauyan gwamnati ya shaida cewa har yanzu ba su mika amsar su ga karar ba.Mai shari’a Ovenseri Aghamieghen Otameri ya dage sauraron shari’ar zuwa Disamba 9, 2025.




