Kungiyar Amnesty International Ta Yi Allah-wadai da Kisan Limamin da ’Ya’yansa 3

Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana matukar damuwarta kan kisan gillar da aka yi wa Limamin Masallacin Juma’a na Maru, Alkali Salihu Suleiman, mai shekaru 79, tare da ’ya’yansa uku — duk da cewa an riga an biya Naira miliyan 11 daga cikin kudin fansar da masu garkuwa da su suka nema, wanda ya kai Naira miliyan 20.
An sace limamin tare da ’ya’yansa ne cikin watan Ramadan a watan Maris. A lokacin da suke hannun ’yan bindigar, kungiyar ta bayyana cewa an dinga azabtar da su, tare da yin amfani da su ta hanyoyi masu ciwo da tauye hakkin dan Adam.
Amnesty ta bayyana cewa hare-haren da ke ci gaba da faruwa a yankunan karkara na arewacin Najeriya sun dade suna faruwa ba tare da matakin da ya kamata daga jami’an tsaro ba.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda babu wani mataki na hukunta wadanda ke da hannu cikin wadannan laifuka, lamarin da ke barin al’umma cikin firgici da rashin kwarin gwiwa.