January 24, 2025

Kuna Son Sanin Zunzurutun Bashin Da Ake Bin Najeriya Yayin Da Matsin Rayuwa Ke Ƙara Ƙamari?

0
images-54.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Bashin da ake bin Najeriya ya kai zunzurutun  naira tiriliyan 134.297 a watan Yunin 2024, kamar yadda Hukumar Kula da Basussuka ta Ƙasa ta bayyana.
 
Da yawan al’umma kimanin miliyan 216.7, wannan yana nufin cewa kowane dan Najeriya na dauke da bashin Naira 619,501, wanda ya ninka sabon mafi karancin albashi na N70,000 har sau tara.
 
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa a kan bashin da kasar ke dauke da shi a karshen zango na biyu na shekara ya nuna gagarumin karin da aka samu a basussukan cikin gida da na kasashen waje.
 
Bashin cikin gida ya kai naira tiriliyan 71.2, yayin da na waje ya kai naira tiriliyan 63.
 
Gwamnatocin jihohi suna da bashin naira tiriliyan 7.1 a waje da kuma naira tiriliyan 4.2 a cikin gida, yayin da gwamnatin tarayya ke da bashin naira tiriliyan 55.8 a waje da kuma naira tiriliyan 66.9 a cikin gida.
 
Wannan karuwar bashi na ci gaba da zama abin damuwa, musamman idan aka yi la’akari da karin naira tiriliyan 13 daga naira tiriliyan 121 da aka ruwaito a watan Maris 2024.
 
Gwamnatin Najeriya na fuskantar matsin lamba wajen rage dogaro da rance saboda damuwar da ake yi kan ingancin tattalin arzikin kasa.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *