Kotun Tarayya ta dakatar da rushe masarautun Kano
![images-4-13.jpeg](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2024/05/images-4-13-1.jpeg)
Daga Abdullahi I. Adam
Bayan sauraron wani koke da Alh Aminu Babba Dan Agundi Sarkin Dawaki Babba, wanda yana daga cikin manyan hakimai a Masarautar Kano, ya shigar a gaban kotun, babbar kotun ta dakatar da rushe masarautun na Kano da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Babban alƙalin kotun Justice AM Liman ya sanya ranar 3 ga watan Yuni domin sauraran ƙarar.
Wasu daga cikin waɗanda muka zanta da su bayan sanar da umurnin da kotun ta bayar sun nuna tsananin jin daɗi, yayin da wasu kuma suke nuna hakan kwata-kwata bai masu daɗi ba.
TCR Hausa za ta ci gaba da kawo maku bayanai kan wannan dambarwa ta masaurun na jihar Kano.