Kotun Taliban ta yi wa wata matashiya bulala 30 a bainar jama’a saboda haramtacciyar soyayya
FILE PHOTO: Taliban forces block the roads around the airport, while a woman with Burqa walks passes by, in Kabul, Afghanistan. August 27, 2021. REUTER/Stringer
Daga Sabiu Abdullahi
Wata kotun Taliban a lardin Faryab na arewacin Afghanistan ta yi wa wata mace bulala 30 a gaban jama’a tare da yanke mata hukuncin watanni shida a gidan yari saboda yin dangantakar haram da kuma guduwa daga gida.
A cewar sanarwar da Babban Kotun Taliban ta fitar a ranar Litinin, an yanke wa matar hukunci ne bisa karya dokokin Afghanistan da ke hana dangantaka ta jima’i a waje da aure.
A wani lamari daban, mutane biyu a lardin Kandahar da ke kudancin kasar sun sha bulala 30 a gaban jama’a tare da hukuncin shekara guda a gidan yari bisa laifin aikata luwaɗi.
Dawowar Taliban mulki a Afghanistan ta kawo ƙaruwar aiwatar da hukunci irin na kisa da bulala a bainar jama’a, musamman ga laifukan kisan kai, fashi da makami, da zina.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta yi kakkausar suka ga amfani da hukuncin bulala da Taliban ke yi, tana mai cewa hakan ya sabawa yarjejeniyar MDD kan hana azabtarwa.
MDDn ta kuma yi kira ga Taliban da su daina amfani da irin waɗannan hukunci.
Amma hukumomin Taliban sun kare matakan nasu, suna cewa hukuncin bulala ya yi daidai da dokokin Afghanistan kuma yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron al’umma.



