January 14, 2025

Kotun Najeriya ta ƙi bayar da belin jami’in Binance duk da ‘rashin lafiyarsa’

0
11_26_31_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A wani zama na kotun tarayya da ke Abuja, babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, wanda ke tsare bisa zargin halasta kuɗaɗen haramun, ya ci gaba da zama a tsare bayan kotun ta ƙi bayar da belinsa.

Lauyan Gambaryan ya shigar da ƙarar neman beli, yana mai bayyana cewa ba shi da ƙoshin lafiya kuma yana buƙatar kulawa daga ƙwararrun likitoci.

Sai dai, Mai Shari’a Emeka Nwite ya ƙi amincewa da wannan roƙo, yana mai cewa akwai likitocin da za su iya ba da kulawa a Nijeriya.

Kotun ta umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta kai Gambaryan asibiti mai inganci a Abuja tsawon sati biyu, tare da rakiyar jami’an tsaro, domin samun kulawar da ake buƙata.

A watan Agusta, matar Gambaryan, Yuki, ta bayyana cewa rashin lafiyarsa yana ƙara tsananta kuma an hana lauyoyinsa su gana da shi tun ranar 26 ga watan Yuli.

Hukumomin Nijeriya sun tuhumi Gambaryan, ɗan ƙasar Amurka da ke aiki a Binance a matsayin jami’i mai kula da bin diddigin badaƙalar kuɗi, tare da Nadeem Anjarwalla, shugaban reshen Afirka na kamfanin daga ƙasar Birtaniya, da laifin halasta kuɗaɗen haramun da suka kai dala miliyan $35.

A watan Maris, kamfanin Binance ya dakatar da hada-hadar kuɗaɗe a Nijeriya, bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na kakkaɓar hanu da masu harkar kirifto, tana mai zarginsu da hannu a hauhawar farashin dala, abin da ya jawo tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *