January 14, 2025

Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Abba Kabir daga gwamna

0
images-2023-11-17T122337.870.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke, inda ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Don haka kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar NNPP kuma gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya shigar.

Gwamnan ya nuna rashin gamsuwa da matakin da karamar kotun ta yanke, ta bakin lauyansa Wole.

Olanipekun, ya bukaci kotun daukaka kara da ta yi watsi da hukuncin kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *