Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamnan Benue Alia, ta kori ƙarar da Titus Uba na PDP ya shigar
Daga Sabiu Abdullahi
A ranar Litinin ne kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke karar da Titus Uba dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ya shigar kan zaben gwamna Hyacinth Alia a jihar Benue.
Hukuncin da mai shari’a Onyekachi Aja Otisi ya yanke, ya yi magana kan wasu muhimman batutuwa guda uku da Uba da PDP suka gabatar, inda daga karshe ya yanke hukunci a kansu.
Da yake watsi da ikirarin Uba na rashin cancantar mataimakin gwamna Samuel Ode, Mai shari’a Otisi ya bayyana rashin samun fom din INEC na EC9 wanda aka yi jabunsa, inda ya tabbatar da cewa akwai bukatar cika ka’idojin doka.
A halin yanzu dai Gwamna Alia me zai ci gaba da zama gwamna a jihar yayin da ɗan takarar PDP kuma yake da damar kai abin zuwa Kotun Ƙoli.