Kotun Ƙoli ta fara sauraren ƙarar Atiku da Obi a kan zaɓen Tinubu
Daga Sabiu Abdullahi
Kotun Ƙolin ta Najeriya ta fara shari’ar ƙararraki uku na ƙalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da ya gabata.
Kotun ta buɗe ne da karar da Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP suka shigar.
Kwamitin mutum bakwai na kotun yana karkashin mai shari’a John Okoro.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Justice Uwani Abba-Aji, Mohammed Lawal Garba, Adamu Jauro, Ibrahim Saulawa, Tijani Abubakar da Emmanuel Agim.
Lauyoyin jam’iyyun suna riga sun bayyana kotun domin gabatar da matsayarsu