January 15, 2025

Kotu ta yi umarnin ƙwace dala miliyan 2 da kadarori 7 na tsohon gwamnan CBN, Emefiele

1
images-26.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin karbe dala miliyan $2.045 da kuma kadarori guda bakwai da aka danganta da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
 
Kadarorin suna wurare masu muhimmanci a Legas, kuma sun hada da dufuleks biyu da aka kammala, filin da ba a gina ba, bungalo, dufuleks mai dakuna hudu, wani babban kamfani da ake ginawa, da kuma gida mai dakuna guda takwas da ke cikin wani gini.
 
Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ce ta nemi umarnin karshe na karbe kadarorin, wanda Alkali Dehinde Dipeolu ya amince da shi.
 
EFCC ta zargi cewa, kadarorin, kudade da hannayen jarin an same su ne daga kudaden da aka samu ta hanyar da ba bisa ka’ida ba da Emefiele ya yi amfani da su wajen sayensu.
 
 

1 thought on “Kotu ta yi umarnin ƙwace dala miliyan 2 da kadarori 7 na tsohon gwamnan CBN, Emefiele

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *