Kotu Ta Yi Fatali Da Umarnin Soke Dawo da Sarki Sanusi

Daga Sabiu Abdullahi
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na soke nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
Kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Mustapha, ya bayyana a hukuncinsa cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayya ƙarƙashin Mai Shari’a Abubakar Liman na ranar 20 ga Yuni, 2024, bai cancanta ba.
Hukuncin da aka soke ya shafi dokar masarautar Kano ta 2024, wadda aka yi amfani da ita wajen sake nadin Sanusi.
A cewar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai Shari’a Liman ya wuce huruminsa wajen soke matakin gwamnatin jihar Kano, wanda aka ɗauka bisa doka ta majalisar masarautu ta 2024.
Haka kuma, kotun ta bayyana cewa karar da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar, wadda Mai Shari’a Liman ya dogara da ita, ba ta da inganci.
Kotun ta ce rashin bin ka’idar shigar da ƙarar ya hana Babbar Kotun Tarayya hurumin yin shari’ar.
A gefe guda, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bayar da umarnin sake duba ƙarar da Sarki Aminu Bayero ya shigar kan hukuncin tsige shi da Gwamna Yusuf ya yanke.
Kotun ta ce akwai hujjojin da suka nuna cewa ba a ba Sarki Bayero damar kare kansa a Babbar Kotun Jihar Kano ba, lamarin da ya sa Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bayyana cewa an gudanar da shari’ar cikin rashin adalci.
Your blog is a testament to your dedication to your craft. Your commitment to excellence is evident in every aspect of your writing. Thank you for being such a positive influence in the online community.SABA303
Hello! I just would like to give a huge thumbs up for the great info you have here on this post. I will be coming back to your blog for more soon.
Very nice post. I just stumbled upon your weblog and wanted to say that I have truly enjoyed browsing your blog posts. After all I’ll be subscribing to your rss feed and I hope you write again soon!
Codzienna dawka sportowych emocji na najwyższym poziomie | Newsy ze świata sportu – piłka nożna, koszykówka, siatkówka i więcej | Sportowe wiadomości z Polski w jednym miejscu | Zostań na bieżąco z wynikami polskich drużyn | Nowoczesny portal sportowy dla każdego fana sportu Sport newsy .