February 16, 2025

Kotu ta yanke wa wani  hukuncin ɗaurin shekaru 14 saboda yi wa ƴarsa ciki

174
images-5-7.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

A wani lamari mai tayar da hankali da ya shafi lalata, wata babbar kotun jihar Bayelsa ta yanke wa Baridapsi Needam mai shekaru 41 hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa diyarsa fyade har ta ɗauki ciki.

Yarinyar dai shekarunta 14 ne kacal a lokacin da abin ya faru, kuma ta haifi diya mace yayin da ake ci gaba da shari’a.

Kotun ta ce ya fara mata cin zarafin ne tun tana da shekaru bakwai kacal kuma aka ci gaba.


Mai gabatar da kara Pere Amanda Egbuson ya gabatar da shaidun da ke nuna cewa wanda ake tuhuma yana jima’i da ‘yarsa tun a shekarar 2020, kuma gwajin DNA ya nuna kashi 99.99 cikin 100 na gaskiya cewa wanda ake tuhuma shine mahaifin yaron da aka haifa.

Alkali D.E. Adokeme ya zartar da hukuncin, inda ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da karar ta ba tare da wata shakka ba, sannan ya yanke hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ga Needam.

Babban lauya mai shigar da kara, Pere Amanda Egbuson, ya yaba da hukuncin a matsayin izina ga wasu, yana mai cewa, “An aika da sako mai karfi cewa kotu ba za ta lamunci irin wadannan munanan ayyuka ba.”

174 thoughts on “Kotu ta yanke wa wani  hukuncin ɗaurin shekaru 14 saboda yi wa ƴarsa ciki

  1. купить диплом государственного образца [url=https://russa-diploms.ru/]купить диплом государственного образца[/url] .

  2. Арматура диаметром 32 мм, изготовленная из стали марки А500С, является одним из самых востребованных видов металлопроката в строительстве. Она применяется при возведении фундаментов, армировании стен и перемычек. https://armatura32.ru

  3. купить диплом о высшем техническом образовании цена [url=https://4russkiy365-diplomy.ru/]4russkiy365-diplomy.ru[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *