January 14, 2025

Kotu ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Aisami hukuncin kisa

3
image_editor_output_image2056816675-1701792605107.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wata babbar kotun jihar Yobe da ke garin Potiskum ta yanke hukuncin kisa ga John Gabriel, sojan da aka sallama daga aiki saboda kashe Sheikh Goni Aisami, wani fitaccen malamin addinin Islama a jihar Yobe.

Bugu da kari, Kofur Adamu Gideon, abokin Gabriel, ya samu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari daga Alkali Usman Zanna Mohammed.

Wannan na zuwa ne shekara guda ke nan bayan sun aikata wannan laifin.

3 thoughts on “Kotu ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Aisami hukuncin kisa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *