Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Wa Matashi Bisa Laifin Kashe Mahaifiyarsa a Kano

Wata Babbar Kotu da ke jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Sagiru Rijiyar Zaki, mai shekara 22, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotu ta same shi da laifin kashe mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa a cikin gida da ke unguwar Rijiyar Zaki.
Mai shari’a ya bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da laifin, lamarin da ya jefa iyalai da al’umma cikin alhini da tashin hankali.
Mutane da dama sun bayyana mamaki da bakin ciki kan wannan lamari, inda suka roƙi Allah Ya kare su daga irin wannan mummunar ƙaddara.