Kotu ta umurci Sadiyya ta yi bayanin yadda aka kashe wasu kuɗaɗe
Babbar kotun tarayyar da ke jihar Legas ta umarci tsohuwar minsitar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan ƙasar na tsawon wata shida.
Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da akla raba akowace jiha.
Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta gurfanar da Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta ‘yancin samun bayanan.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma’a.
Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowane ɗan ƙasa ciki har da SERAP.
Sannan kotun ta kuma umarci ministar ta yi bayanin hikimar biyan naira 5,000 ga talakawan ƙasar miliyan 24.3, wanda adadin kuɗin ya kai kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2021.