Kotu ta tsige kakakin majlisar jihar Bauchi

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Suleiman daga mukaminsa.
An tsige Suleiman ne a matsayin mamba mai wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya a karamar hukumar Ningi ta jihar.
A hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, Kotun daukaka kara ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 10 da ke mazabarsa.