January 14, 2025

Kotu ta soke belin da aka ba wa tsohon akanta-janar Ahmed Idris

12
images-2023-11-14T171150.484.jpeg

Wata kotu da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta soke belin da aka ba wa tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Laifukan da ya yi sun shafi karkatar da kuɗaɗen al’umma da suka kai naira miliyan 109.5, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Mai shari’a Yusuf Halilu na kotun da ke babban birnin tarayya Abuja, ya yanke hukuncin ne bayan Akindele, ɗaya daga cikin wadanda suke shan tuhuma tare da Idris, ya kasa gurfana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar.

Laifukan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gabatar sun hada da tuhume-tuhume 14 da suka shafi sata da kuma karkatar da kudaden gwamnati.

12 thoughts on “Kotu ta soke belin da aka ba wa tsohon akanta-janar Ahmed Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *