December 7, 2025

Kotu ta sake hana belin Nnamdi Kanu

IMG-20240521-WA0014.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Wata kotun tarayya a babban birnin tarayya Abuja, ta sake yin watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan-a-ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, inda lauyoyinsa ke neman kotun ta kawar da umarnin soke belinsa na 2017, bisa zargin tsere wa shari’a.

Haka kuma a yayin zaman sauraron, Maisharia Binta Nyako, ta yi watsi da bukatar Kanu ta neman a kaishi gidan yari na Kuje, idan har aka ki yarda da bukatarsa ta neman beli.

Maisharia Nyako, wadda ta ce kotun ta dade kuma a lokuta da dama tana nazari a kan batun neman belin na jagoran ‘yan a-waren na Biafra, ta ce zabin da ya rage masa kawai a yanzu shi ne ya daukaka kara kan hukuncin.

Ta kara da cewa daga yanzu duk wata bukata da aka sake gabatar wa kotun a kan batun belin, to za ta dauki hakan a matsayin wasa da shari’a.

Daga nan ta umarci Kanun ya mayar da hankali kan fara gudanar da shari’arsa.
Kotun ta dage zaman zuwa ranar 19 da kuma 20 ga watan Yuni domin fara shari’ar.