May 17, 2025

Kotu Ta Miƙa Wa EFCC Kuɗaɗe da Kadarorin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

images-2025-02-21T191036.225.jpeg

Babbar kotun tarayya da ke Legas, a kudu maso yammacin Najeriya, ta yanke hukunci inda ta amince da miƙa wasu kuɗaɗe da kadarori na tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ga hukumar EFCC bayan ƙwace su.

Emefiele, wanda ya jagoranci CBN na tsawon shekaru tara, ya fara fuskantar matsaloli tun bayan sauke shi daga mukami a watan Yuni na shekarar 2023, lokacin da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya tsige shi.

A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Yellim Bogoro ta amince da buƙatar da EFCC ta shigar ta hannun lauya Bilkisu Buhari-Bala, bayan da kotu ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren Emefiele ya shigar don dakatar da shari’ar.

Da wannan hukunci, kotu ta miƙa wa EFCC kuɗaɗen da aka ƙwace daga Emefiele, wanda ya haɗa da dala miliyan 4.7 da naira miliyan 830, tare da wasu kadarori da dama.

Wadannan kuɗaɗe na ajiye ne a bankuna daban-daban, ciki har da First Bank, Titan Bank, da Zenith Bank, inda aka gano sunayen wasu mutane da kamfanoni a matsayin masu su.

Daga cikin kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da:

Gini mai hawa 11 a Ikoyi, Legas;AM Plaza, mai hawa 11, Lekki Peninsula 1, Legas; Imore Industrial Park a Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin, Legas; Mitrewood da Tatler Warehouse a Ibeju-Lekki, Legas; da Gidaje guda biyu a Lakes Estate, Lekki, Legas.