January 15, 2025

Kotu ta mayar da Aminu Bayero a matsayin Sarkin Kano

0
image_editor_output_image1310653016-1718902598120.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin mayar da Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

Kotun ta yi watsi da dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta rusa masarautun jihar Kano guda biyar, har ta kai ga tsige Bayero daga karagar mulki.

Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis.

Wannan lamari dai ya soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke dokar da ta kafa masarautu tare da nada Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15.

Gwamnatin Kano ta dogara ne da dokar da aka soke don tsige Bayero daga karagar mulki ta nada Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14.

Sai dai Aminu Babba Danagundi, wani mai rike da sarauta a tsohuwar masarautar Kano, ya kalubalanci dokar a gaban kotu, inda ya bukaci a bayyana cewa ba ta da tushe.

Hukuncin da kotun ta yanke a yanzu ya mayar da Bayero a matsayin Sarkin Kano, lamarin da ke nuna gagarumin ci gaba a takaddamar da ake yi a kan masarautar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *