March 28, 2025

Kotu ta haramta wa Bayero da  sauran tsofaffin masu sarautu bayyana kansu a matsayin sarakuna

IMG-20240715-WA0008.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wata babbar kotu a jihar Kano ta bayar da umarnin dindindin na hana tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da wasu tsaffin sarakuna hudu yin ikirarin au sarakuna ne a halin yanzu.

Hukuncin ya fito karara ya haramtawa sarakunan Bichi, Rano, Gaya, da Karaye da suka shude tare da ma’aikatansu da wakilansu bayyana kansu a wannan matsayin.

Gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin hana sarautun da aka tsige amfani da mukamansu na sarauta da zama a fadarsu. 

Bugu da kari, gwamnati ta bayar da sanarwar na tsawon sa’o’i 48 ga sarakunan da su bar fadarsu bayan tsige su.