December 7, 2025

Kotu ta hana gwamnatin Kano bincikar Ganduje

IMG-20240515-WA0005.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da kwamitocin bincike da gwamnatin jihar ta kafa domin binciken gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kwamitocin shari’a guda biyu da suke gudanar da bincike kan almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma bacewar mutane tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.

Duk a lokacin mulkin Ganduje, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

1 thought on “Kotu ta hana gwamnatin Kano bincikar Ganduje

  1. It’s acually a nice andd helpful piece of info. I’m
    happy tnat youu simply shuared thiss helpful infformation with us.
    Please kesep uss iformed like this. Thanks ffor sharing.

Comments are closed.