Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago shiga yajin aiki wanda zai iya ɗaiɗaita Najeriya
Daga Sabiu Abdullahi
Kotun kolin masana’antu ta kasa ta dakatar da ƙungiyar kwadago ta Najeriya da sauran kungiyoyi ƴan’uwanta daga shiga yajin aiki.
Kungiyoyin sun bayyana cewa bayan wani taron majalisar zartarwa na kasa da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, sun ayyana yajin aikin gama gari daga ranar 14 ga Nuwamba, 2023.
Kungiyoyin sun dauki matakin ne biyo bayan cin zarafin da suke zargin an yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a makon jiya a jihar Imo.
Sai dai Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyan Tarayya wato Ministan Shari’a sun shigar da ƙara a gaban kotu inda suka nemi kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadagon shiga yajin aikin da suka shirya yi.
Shugaban Kotun, Mai Shari’a Benedict Kanyip, a ranar Juma’a ya umarci kungiyoyin kwadago da su dakatar da yajin aikin da suke shirin yi a fadin kasar.
Yakin aiki irin na ƙungiyoyin ƙwadago an san shi da zuwa da matsaloli iri-iri saboda yadda zai yi tasiri a kowane fannin gudanar da rayuwa a ƙasar, kama daga bankuna, gidajen mai, makarantu, masana’antu da dai sauransu.