Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da ƴarsa
Dgaa Sodiqat Aisha Umar
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika da ‘yarsa Fatima wadanda aka gurfanar da su yau a gaban kotu.
An bayar da belin ne kan kudi naira miliyan 100 ga kowannen su, har da ma sauran mutum biyu da aka gurfanar tare da su.
Ana zargin Sirika ne da sauran mutanen da laifin badakalar kudi da suka kai naira biliyan 2.7.
Sauran ka’idojin belin sun hada da kawo wadanda za su tsaya musu wadanda suka mallaki kadarori a Abuja.