January 15, 2025

Kotu ta bayar da belin ₦300m wa Emefiele

1
BeFunky-collage-82.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A ranar Laraba ne wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.

An bayar da belinsa a kan kudi N300m da kuma mutum biyu masu tsaya masa.

Da yake yanke hukunci kan neman belinsa a ranar Laraba, Mai shari’a Hamza Muazu, ya ce dole ne wadanda za su tsaya masa su kasance suna da takaddun shaidar zama da kuma takardun mallakar dukiya a gundumar Maitama.

Ya kuma umurci Emefiele da ya ajiye dukkan takardunsa da zaibiya amfani da su don yin tafiya a gaban magatakardar kotun, sannan ya ci gaba da zama a Abuja.

Muazu ya ce a ci gaba da tsare tsohon gwamnan na CBN a gidan gyaran hali na Kuje har sai ya cika sharuddan belin.

Emefiele yana fuskantar shari’a bisa zarginsa da laifin zamba.

Tun da farko dai gwamnatin tarayya ta ɗaura tuhume-tuhume 20 na fiye da naira biliyan 6.5 a kan Emefiele.

1 thought on “Kotu ta bayar da belin ₦300m wa Emefiele

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *