Kotu ta ɗaure wani mutumin Bauchi da ya yi wa yarinya fyade a cikin masallaci
Daga Sabiu Abdullahi
Babbar Kotun Jihar Bauchi mai lamba 6 ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Yusuf Bako mai shekaru 50 da haihuwa, bisa laifin yi wa wata yarinya fyade a cikin wani masallaci da ke kan titin Aminu a cikin birnin Bauchi.
Hukuncin ya biyo bayan kama Bako ne a shekarar 2020, a lokacin da ake kan gaɓar kullen COVID-19—laifin da ya amsa.
A baya dai an tsare shi har sau biyu bisa laifukan fyade makamancin haka.
Barista Sha’awanatu Yusuf, darakta mai shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, ta tabbatar da hukuncin a wata hira ta musamman.
Mai shari’a Sa’ad Zadawa na babbar kotu mai lamba 6 ya yanke hukuncin ne a karshen watan Nuwamba bayan kammala sauraren karar da bangarorin biyu suka yi.
Wannan hukunci dai ya nuna jajircewar tsarin shari’a na ganin an hukunta wadanda suka aikata laifi, musamman a lokuta da ake yawan aikata laifuka.