Kotu ta gama zaman sauraron ƙarar Abba Kabir amma ba za ta sanar da hukuncin ba sai daga baya
Daga Sabiu Abdullahi
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta gama shari’a kan ƙarar da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya shigar kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta yi na tsige shi.
Amma kotun ta ce sai daga baya za ta sanar da hukuncin da ta ya ke.
A ranar 20 ga watan Satumba, kotun ta soke kuri’u 165,663 na kuri’u 165,663 na kuri’un Yusuf, lamarin da ya kai ga tsige shi daga muƙaminsa.
Kotun ta yanke hukuncin ne bisa hujjar cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba ta sanya hannu ko tambarin kuri’un da ake magana a kai ba.
Don haka ta ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben gwamnan, wanda hakan ya nuna an yi watsi da nasarar Yusuf.
uwa yanzu dai ana jira kotun ta sake saka ranar ƙarasa wannan hukuncin.