Kotu A Amurka Ta Ba Da Umurnin Fitar Da Bayanan Da Aka Binciko Kan Shugaba Tinubu

Daga Sabiu Abdullahi
Wata kotu a birnin Washington DC na Amurka ta bayar da umarni ga hukumar FBI da ta yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta DEA da su saki bayanan da suka tattara a lokacin da ake gudanar da bincike kan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Alkalin kotun, Beryl Howell, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito. A cikin hukuncin, Howell ya bayyana cewa boye bayanan daga idon jama’a “ba shi da wani ingantaccen dalili kuma ba abu ne mai ma’ana ba.”
Wani dan kasar Amurka mai suna Aaron Greenspan ne ya shigar da karar, yana bukatar kotu ta sake duba hukuncin da ta yanke a baya.
Greenspan ya yi zargin cewa hukumomin tsaron sun karya dokar Freedom of Information Act (FOIA) ta hanyar kasa sakin bayanan da suka kamata cikin lokaci, musamman wadanda suka shafi bincike kan Tinubu da wani da ake kira Abiodun Agbele.
Wannan batu ya sake fitowa fili a lokacin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka kalubalanci cancantar Tinubu a zaben shugaban kasa a Najeriya.
Sai dai kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar tare da tabbatar da nasarar Tinubu.A hukuncin da Alkalin Howell ya yanke, ya ce amsar Glomar da hukumomin FBI da DEA suka bayar – wadda ke nufin musanta ko tabbatar da kasancewar wasu bayanai – ba ta dace ba kuma dole ne a cire ta.