January 15, 2025

Ko a ina Shugaba Tinubu ya ɓoye?

209
WhatsApp-Image-2024-09-12-at-12.12.20-PM-780x470-1

Daga Sabiu Abdullahi  

Ziyarar da shugaba Bola Tinubu ya yi zuwa kasashen ketare da kuma ainihin inda ya ke ya sake zama batun cece-kuce, inda har yanzu ake ci gaba da muhawara.  

Jaridar The Punch a Najeriya ta ruwaito cewa, bayan da Tinubu ya yi tattaki zuwa kasar Sin a ranar 29 ga watan Agusta, kwatsam sai ga shi ya sake bayyana a birnin Landan a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya sa ‘yan Najeriya ke mamakin irin yadda ya yi abubuwan haka a tsakanin wannan lokacin.  

Fadar shugaban ƙasar dai ta yi watsi da bayyana haƙiƙanin inda yake, duk kuwa da sanarwar da ta bayar a ranar 6 ga watan Satumba na bayar da umarnin bayar da agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.  

Masu suka dai na cewa ‘yan kasar na da ‘yancin sanin inda shugabansu yake, musamman a lokutan rikici, kamar matsalar karancin man fetur da ambaliyar ruwa da ta shafi jihohi da dama.  

Yanayin yadda Tinubu yake lulawa manyan biranen kasashen ketare ya jawo ana kwatanta shi da magabatansa, wadanda su ma sun fuskanci suka saboda rashin gaskiya cikin yin hakan.  

Kamar yadda wani mai sharhi ya bayyana, “Ofishin shugaban kasa amintacin jama’a ne a hannunsa, kuma ‘yan kasa suna da ‘yancin sanin inda shugaban yake.”  

Wannan dai ba shi ne karon farko da Tinubu ke yi wa ‘yan Najeriya haka ba, inda a baya-bayan nan ma an ɓoye bayanan tafiye-tafiyen da ya yi zuwa kasashen Faransa da Saudiyya.  

Abubuwan da shugaban ya yi sun haifar da kiraye-kirayen a kara nuna gaskiya da rikon amana a harkar mulki, inda da yawa ke cewa dimokuradiyya na bukatar ta samar da sakamako mafi kyawu.

209 thoughts on “Ko a ina Shugaba Tinubu ya ɓoye?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *