Katsina: Ƴanbindiga sun sace mata da ƙananan yara da dama
Daga Sabiu Abdullahi
Rahotanni da ke fitowa faga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa ƴanbindiga sun kai hari a garin Na-Alma a yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Shashen Hausa na BBC ya ce sun kona gidaje tsre da sace “gomman mutane, galibi mata, har da masu juna biyu, da kananan yara, da wani wanda ‘yan bindiga suka taba sare wa hannu da kafa, bayan kashe wani mai unguwa.”
BBC ta ambato wani mutumin yankin, wanda ya tsallake rijiya da baya yana cewa suna cikin rudani, kuma kashi takwas cikin goma na mutanen garin sun gudu.
Ya ce, “Tun wajen takwas da rabi na dare muka shaida wa jami’an tsaro amman ba su zo ba har sai da mutanennan suka shiga suka fara harbi, sai dai kawai su ce ga su nan zuwa, amman ba su zo ba har sai da ƴanbindiga suka gama kone-kone da duk abin da za su yi sannan suka zo.”
Mutumin ya kara da cewa an yi masu gagarumin ta’adi a harin da ‘yanbindigan suka kai “Asarar kam Allah kadai Ya san yawanta saboda haka suka bi gida-gida suka ƙona kuma duk manyan gidaje ne suka kona sun kuma kashe mai-unguwa.”
Yankin yana ɗaya daga cikin masu fuskantar hare-haren ƴanbindiga fiye da kowane lokaci.
Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ya alaƙanta wannan hari da aka kai garin Na-Alma, da cewa hari ne irin na ramuwar gayya.