January 24, 2025

Kaso 70 na ‘Yan Najeriya Sun Ƙi Bada Cin Hanci a Shekarar 2023—ICPC

0
images-2024-12-03T130812.457.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta bayyana cewa kashi 70% na ‘yan Najeriya da aka nema su bayar da cin hanci a shekarar 2023 sun ki amincewa.
 
Shugaban ICPC, Musa Aliyu, ya bayyana hakan ne bisa ga rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) tare da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Sha’anin Miyagun Laifuka (UNODC) suka fitar kan “Cin Hanci a Najeriya: Yanayi da Tsare-Tsare na 2023.”
 
A cewarsa, “Cin hanci ya fi yawa a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa, hukumomin ‘yan sanda, da kuma hidimomin gwamnati. Amma duk da wadannan kalubalen, abin alfahari shi ne kashi 70% na ‘yan Najeriya da aka nema su bayar da cin hanci a shekarar 2023 sun ki amincewa akalla sau daya.”
 
Ya kara da cewa a yankin Arewa maso Yamma, kashi 76% na wadanda aka bukaci su bayar da cin hanci sun ki amincewa, wanda ke nuna karuwar yaki da cin hanci a wannan yanki.
 
Shugaban ICPC din ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen yaki da cin hanci, tare da kira ga ‘yan kasa su rika kin amincewa da bukatun cin hanci.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *