February 10, 2025

Kasashen Sahel Na Shirin Kafa Kamfanin Jirgin Sama

3
images-2025-02-03T124518.814.jpeg


Ministan Sufuri na Nijar, Kanal Manjo Salissou Mahaman Salissou, ya bayyana cewa ƙawancen kasashen Sahel—Burkina Faso, Nijar, da Mali—na shirin kafa kamfanin jirgin sama don ƙarfafa haɗin gwiwar sabuwar ƙungiyarsu.

Kafar yaɗa labarai ta ActuNiger ce ta ruwaito hakan.

A cewar Ministan, kafa kamfanin jirgin saman na AES (Alliance des États du Sahel) yana da matuƙar muhimmanci, kuma suna shirin gaggauta aiwatar da hakan. Ya ce kamfanin zai kasance da launin kasashen uku tare da haɗa manyan birane da wasu wurare na yankin.

Har ila yau, Salissou ya bayyana cewa shugabannin mulkin soja na Nijar sun umurci hukumomin da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama da su sassauta wasu dokoki domin hanzarta samar da kamfanin jirgin saman yankin.

Tun bayan ficewar su daga ECOWAS, kasashen AES sun ɗauki matakai daban-daban don ƙarfafa haɗin kansu. A baya-bayan nan, sun ƙaddamar da fasfo bai-ɗaya da kuma kafa dakarun haɗin gwiwa don yaƙar ƴan bindiga da ke addabar yankinsu.

3 thoughts on “Kasashen Sahel Na Shirin Kafa Kamfanin Jirgin Sama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *