January 15, 2025

Karyewar darajar naira: Najeriya ta buƙaci Binance ta biya ta diyyar $10B

0
MixCollage-19-Jan-2024-05-15-PM-4209.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci shafin musayar kuɗin intanet na Binance ya biya ta kuɗi dalar Amurka biliyan 10 a matsayin tara.

Wannan na zuwa ne saboda iƙirarin da gwamnatin ta yi na asarar da ta tafka sanadiyyar ayyukan da shafin ke yi.

Wani rahoton BBC Hausa  ya nuna cewa gwamnatin ta zargi Binance da tsawwala farashin musayar kuɗaden waje ta hanyar yin ‘hasashe maras tushe da kuma shaci-faɗin darajar naira, lamarin da ya sa darajar naira ta zube da kimanin kashi 70 cikin 100.’

Wannan ya biyo bayan iƙirarin da Babban Bankin Najeriya ya yi a ranar Talata cewa kuɗi kimanin dala biliyan 26 ne aka yi safarar su ta shafin Binance daga Najeriya zuwa wasu wuraren da ba a sani ba.

Idan ba ku manta ba, a ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa tana tsare da wasu manyan jami’an Binance guda biyu.

A halin yanzu dai jami’an tsaro na ta yi musu tambayoyi bisa zargin shafin da zama wata kafa ta halasta kuɗaɗen haram da kuma samar da kuɗi ga ƴan ta’adda.

Karyewar darajar naira dai na daga cikin dalilan da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya, inda farashin komai ya yi tashi gwauron zabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *