January 24, 2025

‘Kar ka kalli wasan ƙarshe na AFCON idan kana da ciwon zuciya’—Likita

0
images-131.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani Likitan da ke Akure kuma Babban Darakta na Asibitin Sckye, Dokta Thomas-Wilson Ikubese, ya gargadi magoya bayan Super Eagles da masu son kwallon kafa wadanda ke da saurin zuciya da kuma ciwon zuciya da su guje wa wasan karshe na ranar Lahadi.

Mista Ikubese, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Akure, ya ce a maimakon haka ya kamata wadannan nau’ikan mutane su shiga cikin matakan karkatar da tunaninsu.

A halin yanzu dai Super Eagles ta Najeriya za ta kara da mai masaukin baki, Cote D’ivoire, a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON.

Rahotanni sun ce kimanin ‘yan Najeriya hudu ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a yayin da suke kallon wasan kusa da na karshe na Eagles da Afrika ta Kudu a ranar Laraba.

Ikubese ya ba da shawarar cewa irin waɗannan mutane su ɗauki wayar su su bi bayanan kai tsaye, don guje wa kururuwa.

“Zan ba da shawarar cewa kada wannan rukunin mutane su kalli wasan kai tsaye.

“Idan ya zama dole sai sun yi, duk da haka, ya kamata su tsunduma cikin aikin motsa jiki don rage tasirin abin da za su iya fuskanta.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *