January 24, 2025

Kano: Ya kamata a binciki Gwamna Abba Kabir Yusuf, in ji Ganduje

0
images (8) (2)

Daga Sabiu Abdullahi

Wani sabon al’amari ya kunno kai a jihar Kano tsakanin gwamnan Kano na yanzu na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf da kuma tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje a cikin wata sanarwa ya nemi gwamnatin kasar ta gudanar da bincike kan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

BBC ta ruwaito cewa Ganduje ya zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da furta kalaman tunzura jama’a a gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar ‘yan kwanakin da suka gabata a duk fadin kasar, inda ɓangaren gwamnan na Kano ya yi watsi zargin wanda ya kira “soki burutsu”.

Tsohon gwamnan na Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani ne ga zargin da gwamnatin Kano ta yi cewa shi ya yi hayar ƴan daba domin haifar da rikici a jihar a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar.

A cikin sanarwar da Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fitar ranar Alhamis, ya zargi gwamnan Abba Kabir Yusuf da yin kalaman da suka ingiza jama’a ga yin tarzoma da nufin baƙanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An ambato Edwin yana cewa, “Yakamata gwamnatin tarayya ta binciki gwamnatin jihar Kano domin kowa ya san cewa kafin zanga-zangar, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kalamai na tunzura jama’a, saɓani matakan da sauran gwamnonin jihohi suka ɗauka.”

Tun hawa kan mulki, gwamnatin Kano ta NNPP ke takun saƙa da tsohon gwamnan jihar na jam’iyyar APC da ta gada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *